An Fara Babban Taron MDD A Yau Talata

Helkwatar MDD a birnin New York

Makomar Libiya da kafuwar kasar Falasdinu ne manyan batutuwan da za a tattauna a Babban Taron MDD

An fara babban taron MDD na shekara-shekara a yau Talata, inda shugabannin kasashen duniya sama da dari su ka taru don tattaunawa kan matsaloli da batutuwa da dama ciki har da bukatar neman kafa kasar Falasdinu, da makomar Libiya bayan Gaddafi da kuma irin cututtukan da basa yaduwa daga mutum da mutum.

Babban batun da za a tattauna a kai shi ne baiwa kasar Falasdinu kujera a Majalisar Dinkin Duniya, amma za a tattauna kan wasu batutuwan da dama, ciki har da sauye-sauyen siyasa a Libiya. A makon jiya Kwamitin Tsaron MDD ya yi kuri’a da gagarimin rinjaye don mika kujerar Libiya a babban taron ga Majalisar Mulkin Wucin Gadin kasar Libiyar, wanda hakan ke nufin yin na’am da shudewar gwamnatin Gaddafi.

Shugaban Amurka Barack Obama ya isa birnin New York tun da yammacin jiya Litinin tare da cikakken jadawalinsa na taron. Mr. Obama na shirin ganawa da shugaban Majalisar Mulkin Wucin Gadin kasar Libiya Mustafa Abdel Jalil. Mr. Obama zai kuma hadu da shugaban sabuwar kasar Sudan ta Kudu,Silva Kiir. Zuwa karshen wannan makon kuma shugaba Obama zai sadu da Firayim Ministan Isira’ila, Benjamin Netanyahu. Mr. Obama zai yi jawabi ga babban taron na Majalisar Dinkin Duniya a gobe Laraba.

A jiya Litinin Sakatariyar harakokin wajen Amurka da shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff sun jagoranci mata manyan 'yan siyasa sun yi kira da aka kara baiwa mata babbar damar taka rawa a siyasar duniya. A cewar Majalisar Dinkin Duniya yanzu haka matan da ke shugabanci a duniya ba su kai kashi goma a cikin dari ba.

Tun kafin fara taron a hukumance, an fara share fage da taron kwana biyu tun daga jiya Litini, inda aka fi mayar da hankali kan cututtukan da su ka fi kisa a duniya, wadanda kuma ba sa yado daga mutum zuwa mutum.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya yi jawabi a taron inda ya caccaki kamfanonin da ke harkar sayar da kayan abincin da aka sarrafa. Wannan ne karo na biyu da babban taron na Majalisar Dinkin Duniya ya maida hankali kan batun kiwon lafiya. A shekaru goma da su ka gabata Babban Taron ya tinkari cutar AIDS ko SIDA mai karya garkuwar jikin Bil Adama, kuma ya jagoranci samar da ci gaban yin rigakafin cutar da kuma yin jiyyar a duka duniya.

Babban Magatakardan MDD Ban Ki-moon