Wani mai dafa abinci dan kasar Ireland, Alan Fisher, ne ya doke Hilda Effiong Bassey 'yar Najeriya a matsayin wacce ta lashe gasar tseren girki mafi dadewa a duniya, in ji kwamitin Guinness World Records (GWR) a ranar Talata.
Fisher "ya dafa abinci na tsawon sa'o'i 119 da mintuna 57 na ban mamaki a gidan abincinsa da ke Japan," in ji GWR, inda karya tarihin da Hilda ta kafa a watan Mayu.
Idan ba a manta ba, matashiyar ‘yar Najeriyar mai shekaru 26 a duniya ta fara dafa abinci a ranar Alhamis 11 ga watan Mayun na bana kuma ta ci gaba da dafa abincin har zuwa ranar Litinin 15 ga watan mayun banan, inda ta dafa abinci kala dabam-dabam har na tsawon sa’o’i 100 a cikin kwanaki hudun da ta kwashe tana girki babu kakkautawa.
GWR sun ce Hilda wace ta yi niyyar kafa tarihin girki na tsawon sa’o’I 100, ta gaza cima burin nata bayan da aka soke sa’o’I 7 cikin lokacin da ta kwashe tana girki biyo bayan zarcewar lokacin hutun da ya kamata ta dauka a farkon lokacin da ta fara girkin.
GWR sun ci gaba da bayyanai cewa, kamar yadda aka tanadarwa duk wanda zai shiga wannan gasa na girki na dogon zango, an amince ya dauki hutun minti biyar cikin kowani sa’a da zai yi yana girkin.
‘Yar Indiya Lata Tondon ce ta samu kambun gasar ta baya a shekara ta 2019 bayan da ta kwashe sa’o’I 87 da minti 45 tana dafa abinci.