"Ina sane da damuwar mutane da suka zuba jari a wannan lokaci na shekara, na san takaici da zasu shiga, inji Johnson a wani taron manema labarai, amma ya ce babu wata mafita da ya sani".
Johnson ya kakaba dokar kulle mai tsauri bayan da babban jami’in kiwon lafiyar kasar ya tabbatar a jiya Asabar sabuwar barkewar coronavirus a cikin kasar dake yaduwa cikin gaggawa, lamarin da ya kara yawan kamuwa da cutar ba tare da an sani ba.
Dr. Chris Whitty ya fada a wata sanarwa cewa, babu wata shaida dake tabbatar da sabuwar coronavirus tafi yawan kisa ko kuma sabon maganin rigakafin da aka tabbatar ba zai immata ba, amma dai ana kokarin tabbatar da hakan.
Whitty ya ce Birtaniya ta sanar da hukumar kiwon lafiya ta duniya game da sabuwar nau’in cutar, wanda sakataren kiwon lafiyar Birtaniya, Matt Hancock ya fada a ranar Litinin cewa an gano cutar ne a Ingila ta kudu.
Sakamakon sababbin matakan da zasu fara aiki a cikin daren jiya Asabar. mutane dake Landan da kudu maso gabashin Ingila zasu kasance cikin dokar hana fita mai tsauri da zasu shafi kashi daya cikin uku na al’ummar kasar.
Dokar zata bukaci su zauna cikin gida ban da muhimman dalilai, kamar na aiki. Za a kulle shagunan sayar da kaya tare da wuraren shakatawa da cibiyoyin nishadi.