Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 64,520 Suka Mutu Sakamakon Cutar COVID-19 a Kasar Italiya


Kasar Jamus na shirin sake sanya matakan takaita zirga-zirga karo na biyu, yayin da Koriya ta Kudu ke shirin bude karin cibiyoyin gwajin COVID-19 a birnin Seoul.

Ana ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19 da mace-mace a sassan duniya da yawa, lamarin da ya tilastawa gwamnatoci sanya matakan takaita zirga-zirga ko duba yiwuwar daukar matakan kulle don dakile yaduwar cutar.

A nahiyar Turai, Jamus na shirin sake saka dokar kulle a karo na biyu a ranar Laraba, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da cutar ta coronavirus. A cewar cibiyar samar da bayanan coronavirus ta jami’ar Johns Hopkins da ake kira JHU a takaice, ya zuwa safiyar yau Litinin, Jamus ta sanar da samun mutun sama da 1,350,800 da aka tabbatar sun kamu da cutar kuma sama da mutane 22,100 suka mutu.

Yanzu Kasar Italiya ta zarta Birtaniya a matsayin kasar nahiyar Turai da aka fi samun mace-mace, a cewar bayanan cibiyar ta JHU. A safiyar yau Litinin rahotannin sun ce cutar ta kashe mutan 64,520 a Italiya, yayin da ta kashe mutan 64,267 a Birtaniyya.

A nahiyar Asiya kuma, hukumomin kiwon lafiya na Koriya ta Kudu sun ce za a bude cibiyoyin gwajin cutar guda 150 a lokuta dabam-daban a babban birnin kasar, kari kenan aka samu na cibiyoyi sama da 210 da aka bude a kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG