Taron na yini uku na gudana ne a Kano, inda aka zakulo mahalarta su ka fito daga jihohin Kaduna, Katsina, Sokoto da Zamfara da Kebbi da Jigawa da kuma Kano.
A hirar shi da Muryar Amurka, Alhaji Garba Magaji da ya wakilci babban sakataren ma’aikatar ayyukan jinkai da bada agajin gaggawa ta kasa Dr Nasiru Sani Gwarzo ya bayyana cewa, sana'oin da za a koyawa mahalarta taron sun hada da man shafawa, sabulu wanka da na wanki. Bisa ga cewar shi , za a kuma koya masu yadda za su habaka sana'ar noman kifi da hada waya da sauran sana'oi
A nashi bayanin, Dr Biliyaminu Umar kwararren likitan dabbobi dake fama da lalurar ciwon laka kuma shugaban kungiyar masu wannan cuta ta kasa reshen jihar Zamfara yace wani bangare na bitar yayi dai=dai-da fannin daya kware.
Shi kuwa Aliyu Altin Riba shugaban hadaddiyar kungiyar nakasassu ta Najeriya reshen jihar Kebbi yace sun dade suna dakon makamancin wannan tsari daga gwamnati.Ya kuma ce wannan dama ce da masu fama da lalura za su iya tsayawa da kafafunsu, su iya bada gudummuwa ga ci gaban al'umma.
A karshen taron bada horon, za’a baiwa kowane guda daga cikin mahalartan naira dubu 100 a matsayin jari. Sai dai akwai tsarin bibiya daga jami’ai.
Jimlar nakasassu 30 ke halartar taron bitar, wadda za’a kammala a ranar Juma’a .
Duk da cewa, an yi makamancin irin wannan taron a sauran manyan shiyyoyi na Najeriya, amma hakan na alamta cewa, akwai doguwar tafiya kafin wannan shiri na ma’aikatar jinkan da bada agajin gaggawa ya kai ga adadin nakasassun kasar dake bukatar wannan horo da tallafin jari.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5