An Damke Wasu Matasa 'Yan Najeriya Da Miyagun Kwayoyi

Masu Safarar Miyagun Kwayoyi

A jamhuriyar Nijar hukumar ‘yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kama wasu mutane da ake zaton ‘yan Najeriya, ne masu aikin sarrafa wata kwayar ta musamman ta hanyar amfani da hodar ibilis ( COCAINE) da ake kyautata zaton suna sayarwa matasan kasar ta Nijar.

Mutanen uku dukkansu matasa ne hukumar fataucin miyagun kwayoyi ta gabatarwa manema labarai hade da kayan aikin da suke amfani dasu wajan hada wannan kwayar da ruwan kyendir domin yinsa curi curi irin na kuli kuli.

Miyagun Kwayoyi

Kamar yadda Kakakin rundunar ‘yan Sandan kasar Nijar Kaftain Adili Toro Mainasara, ya shedawa manema labarai, yace akan sayadawa matasa wannan kwaya akan Dalar Amurka 50, kimanin Naira 1,800.

Wani matashi dan kasar ta Nijar wanda shima dubunsa ta cika ya shiga hannu ‘yan Sanda dauke da kwayoyi na hadiya fiye da dubu dari da yake sayarwa masu aikin karfi.

Dama jami’an fafutukar yaki da safarar miyagun kwayoyi su gargardi hukumomi da iyayen yara su dage kan maganar tarbiya domin kare matasa daga fadawa mugun hannu bayan da a makon jiya aka kama wasu da ake zargi da laifin kisan kai.

Your browser doesn’t support HTML5

An Damke Wasu Matasa 'Yan Najeriya Da Miyagun Kwayoyi - 2'50"