A jiya Jumu’a ne wakilan Amurka da na kungiyar Taliban ta Afghanistan suka baiwa kansu wani dan gajeren hutu daga doguwar tattaunawar babu kakkautawa.
WASHINGTON DC —
Bangarorin biyu sun kwahse kwannaki 11 suna gudanarwa da wannan doguwar tattaunawa ne a kasar Qatar, inda suke kokarin neman hanyar kawo karshen yakin da suka share shekaru 18 suna gwabzawa da juna a can Afghanistan.
Sai dai kuma wani babban hafsan sojan Amurka ya bayyana cewa sun ci karo da abin da ya kira “wasu ‘yan matsaloli” a lokacin tattaunawar tasu.
Tun daga ran 25 ga watan Fabrariu sassan biyu suka soma wannan tattaunawar a birnin Doha.
Wani jigon Taliban yace a yau Asabar suke dawowa don su ci gaba da taron nasu, inda manzon Amurka na musamman kan samarwa Afghanistan zaman lafiya, Zalmay Khalilzad, yake jagorancin wakilan Amurka.