Ministan harkokin wajen Rasha yace zaman tattaunawa samun zaman lafiya a kasar Syria da aka shirya yi ranar 8 ga watan Fabrairu an tura shi zuwa karshen watan na Fabrairu.
WASHINGTON, DC —
Sergie Lavrov ya bada sanarwar ‘dage zaman a yau juma’a a wajen wani taro a Moscow da akayi da wasu kungiyoyin yan tawayen Syria.
Lavrov bai bayyana dalilin da yasa aka dage tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya zata shiga tsakani a Geneva ba.
A farkon wannan makon, Turkiya da Rasha da kuma Iran sun kawo wasu wakilan daga gwamnatin Syriya da kuma kungiyoyin Yan tawaye zuwa Kazakhstan domin yin wani zagaye na shawarwarin samun zaman lafiya da ya kare, inda kasashe guda uku suka amince zasu taimaka wajen sa’ido akan tsagaita wuta da kuma yin aikin, magance rikicin Syria a siyasance .