An Dage Zaben Raba-Gardama A Ghana

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya sanar da dage zaben raba-gardama na ranar 17 ga watan Disamban 2019.

Shugaban ya fada a cikin wani jawabi da ya yiwa kasa ta telbijin da yammacin jiya Lahadi, an dage zaben domin kara tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma wayar da kan al’umma game da muhimmancin zaben.

Za a gudanar da zaben raba-gardamar ne domin yiwa dokar kasa gyaran fuska ta yadda jami’iyyun siyasa za su zabi shugabannin hukumomin birane da na gundumomi da ma wakilan majalisun kananan hukumomi.

Sai dai batun saka siyasa a wurin zaben wakilan majalisun kananan hukumomin shine yafi daukan hankali a cikin gangamin da babbar jami’iyyar adawa ta National Democratic Congress (NDC) ke yi cewa kada ‘yan kasar su zabi amincewa da gyaran fuskar.

Hakan ya yi sanadiyar shugaban kasa ya janye kudurin dokar domin samun karin wayar da kan masu kada kuri’a su fahimci bukatar yiwa dokar kasa mai aya ta 55 a kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1992 gyaran fuska.

Nasarar yiwa dokar gyaran fuska zai ba jami’iyyun siyasar kasar damar tsayar da masu takara da zasu shiga zaben shugabannin hukumomin birane da na gundumomi.

Gwamnati na bukatar akalla kashi 40 cikin dari na wadanda suka cancanci yin zaben su kada kuri’a kana tana bukatar kashi 75 cikin dari na wadanda zasu kada kuri’ar su zabi amincewa kafin ta kai ga samun nasara.

A cikin hirarshi da Sashen Hausa, Mohammed Naziru Seidu, babban jami’in sadarwa na babbar jami’iyyar adawa ta NDC, ya ce shugaban kasar ya tsorata ne ganin ‘yan Ghana ba zasu goyi bayansa ba a wannan zabe.

Saurari cikakkar tattaunawarsu da Baba Yakubu Makeri:

Your browser doesn’t support HTML5

An Dage Zaben Raba-Gardama A Ghana