Wata kotun mulki a kasar Uganda ta tabbatar da wata doka wacce ta cire kayyade shekaru tsayawa takara akan shuwagabannin kasar, abin da ya bawa dadadden shugaban kasar Yoweri Museveni damar ci gaba da kasancewa a mulki.
Bayan muhawarar sa'oi 11, hudu daga cikin biyar na manyan alkalan kotun tsarin mulkin Uganda sun soke wata doka da ke hana wanda ya kai shekaru 75 zama shugaban kasar.
A da Museveni, mai shekaru 73 bai cancanta ya sake tsayawa takara ba idan wa'adin shi ya cika a shekarar 2021.
Masu sukar lamiri da dama basu goyi bayan dage iyakar shekarun ba inda suke cewa mulkin Museveni na shekaru 32 na cike da cin hanci da rashawa da take ‘yancin bil'adama da kuma rashin abubuwan more rayuwa.