An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Isra’ila Da Falasdinu

Rokokin da Falasdinu suka harbawa Isra'ila.

Isra'ila da kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Falasdinu a zirin Gaza sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da yammacin Asabar, domin kawo karshen arangamar da aka shafe kwanaki biyar ana yi, wadda ta kuma yi sanadin mutuwar Falasdinawa 33 da suka hada da kananan yara da kuma mutane biyu a Isra'ila.

Bayan da kasar Masar ta shiga tsakani, yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki ne bayan karfe 10 na dare. Inda aka samu musayar wuta da rokoki a cikin mintuna na karshe da kuma hare-haren da Isra'ila ta kai na tsawon mintuna da dama da suka wuce wa'adin.

Wani jami'in kungiyar Falasdinu ya ce rawar da Masar ta taka na shiga tsakani na da matukar muhimmanci wajen cimma wannan yarjejeniya.

Yarjejeniyar dai ta hada da tsagaita bude wuta da Isra'ila da Falasdinawa suka yi da kuma kawo karshen hare-haren da ake kai wa fararen hula da gidaje.

Masar ta bukaci bangarorin biyu su kiyaye tare da aiwatar da bin ka’idojin yarjejeniyar tsagaita bude wutar.

Sai dai yarjejeniyar ba ta tabo batutuwan da suka haifar da yakin baya-bayan nan tsakanin Isra'ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa a zirin Gaza ba.