An Cimma Daidaito Kan Matsawa Koriya ta Arewa Lamba

Wannan hoton da ma'aikatar tsaron Koriya ta Kudu ta bayar ya nuna wata bindigar igwa samfurin K-9 155mm tana maida martani ta hanyar bude wuta kan Koriya ta Arewa daga tsibirin Yeonpyeong.

Yau Laraba ne kuma manyan mashawartan makaman nukiliya na Amirka da Koriya ta kudu da kuma kasar Japan suka cimma daidaituwa a wajen wani taro da suka yi na bukatar dake akwai na kara matsawa Korea ta arewa lamba da aza mata takunkunmi,

yayinda kuma zasu ci gaba da daukan matakan diplomasiya domin tinkarar shirin nukiliyan kasar.

Wakilin Amirka na musamma akan manufofin Koriya ta arewa Sung Kim ya fada bayan shawarwarin da suka yi a birnin Soul cewa niya ko kuma take taken Korea ta arewa a fili suke.

Yace tilas su nuna damuwa akan wannan al'amari.

An yi wannan taron ne bayan da Korea ta arewa ta yi ikirarin cewa ta samu ci gaba ta farnin shirin nukiliyarta, kasar da ta yi shekara da shekaru tana barazana cewa zata kaiwa Korea ta kudu da Japan da kuma Amirka hari da makaman nukiliya.

Kasashen uku suna cikin shawarwarin da kasashen shidda suka yi akan batun lalata muggan makamai domi tinkarar dimbin makaman nukiliyan da Korea ta arewa ta tara, taron da bai yi nasara ba.