Wannan zanga-zanga ana yin ta ne akan Cin Hanci da Rashawa kuma an ci gaba da yinta bayan gwamnati ta farfado daga zaben rashin tabbas. A wajen kasashen yamma kuwa, wannan rikici wani abu ne da ya zamo tsaka mai wuya sakamakon mutane akan titunan Bucharest na bankado mummunan asirin gwamnati na cin hanci da rashawa, wanda Gwamnatin Amurka da kuma Tarayyar Turai suka yabawa.
Ga wasu daga cikin masu yin wannan zanga-zanga dai, na ganin cewar masu yaki da cin hanci da rashawar sun zamo bata gari da kansu. Wanke laifin almundahanar kasa da Dalar Amurka dubu $50,000 a matsayin ba laifi ba ya batawa mutane rai matuka.
Wanda gwamnatin dai ta janye dokar daga baya, amma duk da haka an cigaba da zanga-zangar, da yawa daga cikin mutanen kasar sun yarda cewa shuwagabanninsu na amfani da dokokin dake yaki da cin hanci da rashawa wajen muzgunawa abokanan hamayya kamar yadda gwamnatin kwaminisanci ta tsohon shugaba marigayi Nicolae Ceausescu.