Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tillerson Ya Tattauna Da Takwarorin Aikinsa Na G-20


Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson (Tsakiya) da wasu takwarorin aikinsa
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson (Tsakiya) da wasu takwarorin aikinsa

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya halarci babbar taron kungiyra kasashemafiya karfin tattalin arziki na G-20 a karon farko tun bayan da ya karbi ragamar wannan aiki.

A bayan tattaunawar da za a yi ta kungiyar, an shirya Tillerson zai gana da ministocin harkokin wajen wasu kasashe, ciki har da na Birtanyia da Turkiyya, Italiya, Korea ta Kudu, Japan da kuma Brazil.

Amma babbar tattaunawar da zai yi a gefen wannan taro na G-20 ita ce ganawar da zai yi da ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov.

Shugaban Amurka Donald Trump, yana fifita manufar harkokin wajen da za ta fifita muradun Amurka kan komai, musamman a fannonin cinikayya.

Ministan harkokin wajen Saudia, Adel al-Jubair, ya fada kafin ganawarsa da Tillerson cewa kasarsa ta na dokin yin aiki tare da gwamnatin Trump a kan dukkan batutuwa, kuma ta na da kwarin gwiwar za a iya shawo kan dukkan matsalolin da ake fuskanta a yankin gabas ta tsakiya.

XS
SM
MD
LG