KEBBI, NIGERIA - A jihar kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya ne jami'an hukumar hana fasa kwabri ta kama wasu mutane da suka kashe Jakuna da kuma safarar naman su abinda kwantorolan hukumar Joseph Attah ya ce ya sabawa doka.
Wannan na zuwa ne lokacin da masana ke ganin cewa yawan take dokoki da ake yi baya rasa nasaba da abinda ya jefa kasar cikin kalubale ta fuskoki daban daban abinda ke kara jefa ‘yan kasa cikin kuncin rayuwa.
A halin da ake ciki yanzu rayukan ‘yan Najeriya musamman talakawa na ci gaba da fuskantar halin kunci sanadiyar matsaloli da suka yi wa kasar kaka-gida kama daga matsalar rashin tsaro, tsadar abinci, tsadar man fetur, rashin wadatattar wutar lantarki da dai makamantan su.
Wannan kuma bai hana ‘yan kasar rufe idanu suna aikata wasu ayukka da dokokin kasa suka hana ba, ba tare da la'akari da illolin da yin hakan kan iya haifarwa ba.
Aminu Salihu direban motar tirela da ta dauko naman jakunan ya ce baya da masaniya akan ko menene ya dauko. Shi kuwa wanda ke rike da naman Sylvester ya ce sako ne kawai aka bashi ya isar.
Jama'a dai na ganin da ‘yan Najeriya shugabanni da wadanda ake shugabanta zasu mutumta dokokin kasa da al'amurra za su gudana yadda ake muradi.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5