An Ceto ‘Yan Gudun Hijirar Rohingya 382 Daga Kan Tekun Bangladesh

Indonesia Rohingya Boat People

An ceto akalla ‘yan gudun hijirar kabilar Rohingya 382 a gabar tekun Bangladesh, bayan da igiyar ruwa ta karkatar da kwale-kwalen kamun kifin da suka yi cunkoso a cikinsa.

Dogarawan tsaron bakin teku sun ce da yammacin jiya Laraba ne suka hango kwale-kwalen sannan suka janyo shi zuwa bakin teku. Wani hoton bidiyo da wani dan jarida ya dauka ya nuna tarin 'yan gudun hijirar da galibinsu mata ne da kananan yara da suka nuna alamun tagayyara a lokacin da ake fito dasu daga kwale-kwalen.

Ana kyautata zaton daga Bangladesh kwale-kwalen ya taso akan hanyarsa ta zuwa Malaysia amma aka tuso keyarsa saboda tsauraran matakan da aka dauka na kare bakin iyakokin kasar sakamakon annobar cutar coronavirus. Wani dogarin tsaron bakin teku ya ce kusan tsawon watanni biyu kwale-kwalen ya yi kan teku kuma fasinjojin cikinsa sun yi fama da matsananciyar yunwa.

Kusan ‘yan Rohingya miliyan daya ke cunkushe a sasanonin ‘yan gudun hijira masu matsatsi kuma cike da kazanta a kudancin Bangladesh, galibinsu daga Myanmar suka tsallako don gujewa mummunan farmakin sojojin kasar a shekara ta 2017.