Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: China Ta Ce Hana Hukumar WHO Tallafin Kudade Zai Shafi Kasashe


A yau Laraba China ta fadi cewa matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na hana bada kudaden tallafi ga hukumar lafiya ta duniya ta WHO zai shafi kasashen duniya gaba daya a yayin da suke kokarin kawar da annobar cutar coronavirus.

Wadannan kalaman daga ma’aikatar harkokin wajen kasar na zuwa ne bayan sanarwar da Trump ya yi a ranar Talata inda ya ce hukumar WHO ba ta yi cikakken binciken da ya kamata ba a rahotonnin farko da ta bayar na bullar cutar a China.

Ita ma kasar Jamus ta bi sahun masu kare hukumar, yayin da a yau Laraba Ministan harkokin wajen kasar, Heiko Maas, ya fadi cewa dora laifi akan wani "ba zai taimaka ba."

Akwai kusan mutane miliyan biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin duniya, to amma saboda matsalar karancin kayan gwajin cutar a yankuna da dama, ana ganin adadin ya fi haka. A yau Laraba wata kididdiga da jami’ar Johns Hopkins ta fitar ta nuna cewa adadin wadanda suka mutu a fadin duniya ya haura mutane 126,000.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG