An Ceto Wasu 'Yan Mata Da Aka Yi Yinkurin Safararsu Zuwa Saudiyya

Wasu 'Yan Mata Da Aka Ceto Kafin Sarrafar Dasu Ga Saudiyya

Hukumar yaki da safarar mata da kananan yara ta NAPTIP, ta kama wasu 'yan mata kan hanyarsu ta zuwa kasar Saudiyya, a babban filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.

Shekarun wadannan 'yan mata 14, 15, 18 da kuma 21 ne, kuma
wani mutum, wanda shi ne aja dinsu na zuwa Saudiyya, da ke jagorantarsu yayin da aka cafke su a filin jirgin saman, ya kubuce, ba a kama shi ba.

Wasu 'Yan Mata Da Aka Ceto Kafin Sarrafasu Ga Saudiyya


Da ya ke bayani, shugaban Hukumar, Abdullahi Lawali, ya ce da aka same su, an kai su Katsina, inda nan ne aka yi musu fasfo, bayan haka, sai aka maida da su Damagaram.

Ya ce yanzu haka cibiyar ta dauki nauyin wadannan 'yan mata kafin iyayensu da aka tuntuba su zo su tafi da su.

Wasu 'Yan Mata Da Aka Ceto Kafin Sarrafasu Ga Saudiyya


Wasu ma'aikatan hukumar sun tattauna da 'yan matan, domin sanin matsalolinsu, da kuma wayar musu da kai game da illolin irin wannan tafiye tafiyen.

A na ta bangaren, shugabar kungiyar da ke yaki da musguna wa mata, Hajiya Umma Dine, ta ce za su bi diddigin wannan matsalar, da kuma samar da hanyoyin fadakar da iyayen yaran hakkin da ya rataya a wuyansu, tare da kwato musu hakkinsu.

Saurari rahoto cikin sauti daga wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari.

Your browser doesn’t support HTML5

An Ceto Wasu 'Yan Mata Da Aka Yi Yinkurin Safararsu Zuwa Saudiyya