Wannan yunkurin hankade gwamnatin Mahamadou Issoufou na zuwa ne dai dai lokacin da siyasar Nijar ta yi zafi kowane dan takarar shugabancin kasar na ta yakin neman zabensa.
Wasu masu adawa da shi shugaban mai ci yanzu, suna ganin ba abinda ya tsinanawa kasar, hasalima sai koma baya data ke dada samu.
To amma magoya bayan Issoufou na ganin wannan kawai adawa ce ta jam’iyyun da basu da mulki a hannu don yin amfani da haka su nemi kuri’un mutanen kasar.
A makon da ya gabata ne dai aka kai samamen yin juyin mulkin amma ya kasa kaiwa ga gaci, sakamakon haka ne wadannan kame-kamen wasu manyan Sojojin kasar ya biyo baya.
Ya zuwa yanzu dai ba wani farar hula a Nijar da aka kama bisa wannan zargi na hambarar da zababbiyar gwamnatin farar hula a kasar. Za ku ji sunayen wadanda aka cafke din a cikin rahoton kasa daga Wakilinmu a Yamai Sule Mumuni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5