Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Najeriya Sun Kuduri Fahimtar Juna Da Kungiyoyin Addinai


Gwamna Abdul'aziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya
Gwamna Abdul'aziz Abubakar Yari na Jihar Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya

Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari na daya daga cikin gwamnonin Najeriya da suka yanke shawarar yin aiki kafada da kafada don fahimtar yanayin tsaro da tabbatar da shi.

Musamman bayan la’akari da abinda ya faru a tsakanin mabiya Shi’a da Sojojin kasar a Zaria. Inda ya bayyana irin matakan da suke son dauka don kiyaye faruwar irin wannan lamari anan gaba.

Ya bayyana yadda ake samu karancin fahimta tsakanin gwamnatoci da kungiyoyin addinai a Najeriya wanda suke ganin yana taka rawar gani sosai wajen kawo matsalolin rashin tsaro a cikin kasar.

Ya kara da cewa, babbar bukatarsu itace, su kafa dokoki a jihohinsu don tabbatar da bin doka da oda daga jami’an gwamnati har zuwa kan mutanen gari. Ta yadda duk wanda ya taka doka doka zata taka shi domin tabbatar da adalci.

Malam Abdulaziz Yari yace nan gaba kadan za su tattauna da jami’an tsaro don ganin yadda za a dinga aiki tsakani da Allah don tabbatar da duk wani abu da ka iya tasowa da ya shafi tsaro an yi abinda ya dace ba tare da kunbiya kunbiya ba.

Daga karshe yayi kira ga ‘yan jarida da su yi aiki bisa kishin kasa da zummar yayata abubuwan daza su kawo zaman lafiya da fahimtar juna ba tada hankalin al’umma ko zuga su ta hanyar rahotannin da ka iya dama lissafinsu ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG