Hukumomi a Jamhuriyr Nijar sun bada sanarwar karawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar hurumi ta yadda za ta gudanar da aikinta ba sani ba sabo wajen farautar mahandaman dukiyar jama’a.
Taron majalisar ministoci na ranar Juma’ar da ta gabata ne ya bada sanarwar kaddamar da sababbin dabarun yaki da cin hanci da rashawa da nufin karawa hukumar karfi.
A cikin hirarsu da Sashen Hausa, Mai Shari’a Abdulrahamu Usman, shugaban hukumar yaki da cin hanci na Jamhuriyar Nijar, ya bayyana cewa wannan sabuwar dokar ta ba hukumar izinin kama dukiyar mutum ta rike har sai an kammala bincike. Har ila yau, dokar ta bada izinin shiga gidan mutum a gudanar da bincike da kuma hana mutum fita kasar sai an san inda yayi da dukiyar kasa.
Duk da yake kungiyoyin kare hakin bil’adama suna cewa ba girin-girin ba tayi mai, sun yaba da daukar wannan matakin. Sai dai sun kalubalanci hukumar ta fara da kama wadanda suke kusa da shugaban kasa da ake zargi da rubda ciki da dukiyar talakawa.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Sule Mummuni Barma ya aiko daga birnin Niamey:
Your browser doesn’t support HTML5