An Bukaci Majalisar Dattawa Ta Sake Salon Yadda Ta Ke Aiki

Shugabannin Matasan Arewa

Bayan sun tashi daga wani babban taro da suka yi a birnin Abuja dake Najeriya, shugabannin kungiyoyin matasan arewa sun ce za su yi wata zanga zangar da ba'a taba yin irinta ba a Najeriya idan 'yan majalisar dattawa ba su sauya salon yadda suke gudanar da aiayyukansu ba.

Shugaban matasan na jihohin arewa 19 tara Imrana Wada Nas shi ya bayyana hakan bayan taron nasu.

Wada ya zargi 'yan majalisar da cewa suna ma shugaban kasa zagon alhali kuwa yawancinsu ta dalilinsa suka samu zuwa majalisar.

A 'yan kwanakin nan an yi taki ruwa rana tsakanin Majalisar Dattawan ta Najeriya da mukaddashin shugaba hukumar EFCC Ibrahim Magu da kuma shugaban hukumar kwastam Hameed Ali.

Wannan takaddama ta sa an kasa tabbatar wa da Magu mukaminsa yayin da shi kuma Hameed Ali bai samu kyakyawan iso ba bayan da ya bayyana a gaban majalisar babu kayan sarki kamar yadda aka bukaci shi ya yi.

Sannan a farkon makon nan ne aka kori shugaban marasa rinjaye Sanata Ali Ndume bayan da ya ta da batun cewa Sanata Dilo Malaye ya na amfani da takardar shaidar karatu ta bogi yayin da shi kuwa Shugaban Majalisar Bukola Saraki ake zargin ya shigo da mota ba tare da ya biya cikakken kudin kwastam ba.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bukaci Majalisar Dattawa Ta Sake Salon Yadda Ta Ke Aiki- 3' 13"