An Bukaci Gwamnati da ta Zakulo Masu Kashe Shugabannin Addini

Shugaban kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Iqamatis Sunnah ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau

Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya fada a jarshen taron hadin kan kasa na Kungiyar Izala a Lagos cewa yin haka ne zai sa jama'a su yarda da gwamnati.
Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'ah Wa Iqamatis Sunna ta Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta bankado mutanen da suke kashe shugabannin addini a kasar, domin maido da martabarta a idanun jama'a.

Sheikh Bala Lau, ya fada a wajen taron hadin kan kasa da wa'azi da ya samu halartar wakilai daga kasashen Afirka ta Yamma da dama a Lagos cewa muddin ba a yi haka ba, to sauran shugabannin addini da ma wasu shugabanni a kasar ba su tsira daga farmakin wadanda ke aikata wannan ta'asar ba.

Shugaban na kungiyar Izala a Najeriya, yace malamai abokan aikin wanzar da zaman lafiya a cikin kasa ne, kuma muddin su na fuskantar farmaki, to al'umma ce take fuskantar farmaki.

Sheikh Bala Lau ya bukaci da a mika musu rahoton binciken da aka yi kan kisan Sheikh Ja'afar Mahmud da aka yi shekara da shekaru da suka shige ba tare da bayanin abinda ya faru ba, da kuma na Sheikh Muhammad Awwla Albani wanda aka kashe kwanakin baya a Zariya.

Mataimakin shugaban Najeriya, Namadi Sambo, shi ma yayi jawabi ga taron inda yake cewa ba za a taba samun ci gaba a kasa ba, sai idan akwai zaman lafiya da hadin kai.

Gwamnan Jihar Osun, Alhaji Ra'uf Aregbesola, yace dole a rika kai zuciya nesa, idan ba haka ba kuwa, sabani da rikicin addini ba zai kare ba.

Wannan taro da kungiyar Izala ta shirya, yana samun halartar wakilai mabiya addinai dabam dabam, kuma ana gudanar da shi ne a Lagos.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnati ta yi kokarin Gano Masu Kashe Shugabannin Addini - 2:17