Majalisar matasan ta ce daukar wannan matakin zai kasance wani babban yunkuri na dakile matsalar tsaro da ke addabar daukacin ‘yan kasar baki daya.
Wata sanarwa da majalisar ta fitar dauke da sa hannun mataimakin shugabanta na shiyyar kudu maso yammacin Najeriya Kwamared Dotun Omoleye, ta ce ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda ya zama wajibi, musamman yanzu da sace mutane domin karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a kasar.
Karin bayani akan: jihar Zamfara, Kaduna, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Majalisar matasan ta bayyana damuwarta akan yadda a yanzu ‘yan bindigar suka raja'a wajen sace dalibai a makarantu da kuma wasu wurare, duk kuwa da matakan da gwamnatin tarayya ta ce tana dauka akan su.
Sanarwar ta bayyana rashin tasirin kalaman shugaba Buhari da ya ce satar daliban makarantar sakandaren Jangebe a jihar Zamfara shi ne zai zama na karshe, inda ta ba da misali da hadisar da auku a baya-bayan nan ta sace wasu dalibai 39 na kwalejin nazarin gandun daji ta Mando a garin Kaduna a ranar Alhamis da ta gabata.
A cewar majalisar, a halin da ake ciki yanzu “’yan Najeriya ba su da tsaro da kwanciyar hankali a gidajensu da makarantu, da wuraren aikinsu, akan tituna, har ma a gonakinsu na noma.”
Majalisar matasan ta jinjinawa dakarun tsaron Najeriya akan jajirjewarsu wajen yaki da ‘yan ta da kayar baya, duk da yake ta bayyana tababa akan tasirin umarnin shugaban kasa na harbe duk wanda aka gani da bindigar AK-47 ba bisa kaida ba.
Ta ce “muddin ba’a tabbatar da ayyana ‘yan bindigar a matsayin ‘yan ta’adda ba, ba wani tasiri da wannan umarnin zai yi.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda, shi zai bayar da damar daukar wasu tsauraran matakai akan duk wani bata-gari da aka kama da ta da zaune tsaye.
Kalu balen tsaro na ci gaba da uzzura a kasar ta Najeriya musamman a yankin Arewa, inda ‘yan bindiga suka karkata wajen sace dalibai a makarantun gwamnati na kwana.
Na baya-bayan na shi ne sace dalibai 39 a kwalejin nazarin gandun daji ta Mando a garin Kaduna a makon nan da ya shige, wadanda har kawo lokacin hada wannan labarin ba’a sako su ba, duk da yake jami’an sojin kasar sun ce sun dakile wani yunkuri na sace wasu daliban a wata makarantar sakandare a Kaduna a karshen mako.
Ku Duba Wannan Ma An Dakile Yunkurin Sace Daruruwan Daliban Sakandare A Kaduna Ku Duba Wannan Ma Daliban Kwalejin Da Aka Sace a Kaduna Sun Nemi Gwamnati Ta Kai Musu Dauki