An Bukaci Amurka Da Iran Su Kai Zuciya Nesa

Iran

Wasu Kasashen Yamma dake kawance da Amurka da suka hada da Faransa, Jamus, da Birtaniya sun bukaci sulhu tsakanin Amurka da Iran.

Kasashen Turai kawayen Amurka sun yi kira ga bangarorin biyu na Amurka da Iran da su maida wukaken su kube, biyo bayan alwashin da Iran ta yi na maida martani a kan kisan babban kwamandan ta Qassem Soleimani da Amurka ta yi a Iraqi.

Zanga-zanga ta barke a duk fadin gabas ta tsakiya, a daidai lokacin da kungiyar NATO ta jingine shirin horarwa a Iraqi, a yayin da ake kara fargabar yaduwar tashe-tashen hankula.

Duk da yake Amurka ba ta sanar da kawayen na ta na turai ba kafin kai harin akan kwamandan na Iran, Prime Ministan Britaniya Boris Johnson, ya ce kasar sa “ba za ta yi alhinin mutuwar Soleimani ba”.

Ba Amurka kadai ba, Britaniya ma na cikin kasashen da suka ji jiki a hannun sa, in ji Darakta-Janar na cibiyar ayukan gidan sarautar Britania, Karen von Hippel.

Qassem Soleimani ne ke da alhakin mutuwar daruruwan sojojin Amurka da wasu kasashen yammaci, ciki har da Britania”.

Kasashen Britania da Faransa da Jamus, a jiya Litinin sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa, inda suke kira ga bangarorin 2 da su kai zuciya nesa su kuma nuna halin dattako.

Kungiyar Tarayyar Turai ta E.U, ta gayyaci ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif zuwa Brussels, a kokarin ganin an dakile rikicin.