'Yan kwanaki bayan kisan Janar Qassem Soleimani, na kasar Iran sanadiyar wani harin sama da Amurka ta kai a Iraq, masu fashin baki a kasashen duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu, game da abinda lamarin ka iya haifarwa.
A wata hira da Muryar Amurka ta yi da Farfesa Djibo Hammani dake jamhuriyyar Nijar, ya ce bayan kisan Soleimani, barazanar da Amurka ta yi akan sake kai hari a yankin da ‘yan Shi’a su ke, babban abun damuwa ne. Wadannan ‘yan Shi’ar ‘yan kasar Saudiyya ne, kuma a yankinsu rijiyoyin danyen mai su ke.
Wannan sabuwar barazanar ta Amurka ga Iran, ta sa jama’a a ko ina juyayi, da nuna damuwa ganin cewa idan haka ta faru, kasar Saudiyya zata shiga cikin lamarin, kuma yaki na iya barkewa, yaki idan an san farkon sa, ba a san karshen sa ba.
Ga karin bayani cikin sauti.
Shi ma Farfesa Usman Bugaje ya bayyana irin ta shi fahimtar, yakin duniya na farko da na biyu, duk irin wadannan abubuwan ne suka janyo su.
Ba a fatan haka ta faru tsakanin Amurka da Iran, domin idan yaki ya barke tsakanin su, ba Amurka da Iran kadai ne za su wahala ba, kusan duk kasashen duniya abin zai shafe su.
Farfesa Bugaje, ya na ganin cewar alakar kasashen duniya za ta karu, domin zata hada kan wasu, ta kara masu karfi, ta kuma raba kan wasu.
Ga hira da Farfesa Usman Bugaje cikin sauti.
Facebook Forum