An Bude Wuraren Ibada a Abuja Bisa Wasu Sharudda

Biyo bayan sassuta dokar kulle da mahukuntan Najeriya suka yi don yaki da cutar COVID-19, mahukuntan Babban birnin Tarrayar Najeriya sun bada izinin bude Masallatai da Majami'u bisa jerin wasu sharuddodi.

Kamar yadda ma'aikatar raya birnin ta sanar, dole ne kowane wurin ibada ya tanadar da ruwan wanke hanu da sabulu da man kashe kwayoyin cuta, kowane mai ibada kuma dole ne ya sanya takunkumin fuska da bada tazara yayin ibada, sannan kar a wuce awa daya a wurin ibadar. Da dai sauran ka'idoji masu yawan gaske.

Duk da haka, shugabannin musulmi da kirista a birnin sunyi na'am da wadannan ka'idoji.

Kamar yadda suka shaidawa Muryar Amurka, shugabannin addinan sunce dama can addinan suna koyar da tsafta don haka wannan ba wani sabon abu bane.

Yanzu dai abin jira a gani shine yadda masu ibada zasu bi wadannan ka'idoji da sharrudda da aka gindaya masu kafin lokaci da kuma bayan ibadar.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bude Wuraren Ibada a Abuja Bisa Wasu Sharadodi - 3'14"