An Bude Gasar Karatun Alkur’ani Mai Girma Da Gidan Talabijin Din Gaskiya Ya Shirya

GASAR KARATUN ALKUR’ANI MAI GIRMA DA GIDAN TALABIJIN DIN GASKIYA YA SHIRYA

An bude gasar karatun Alkur’ani mai girma da gidan talabijin na Gaskiya mai cibiya a Ghana ya shirya a babban birnin Najeriya Abuja.

Gasar wacce a ka fara daga matakin jihohi, ta shafi dukkan jihohin arewacin Najeriya 19 in ban da Kwara.

Jagoran gasar Dr.Abdulkadir Saleh Kazaure ya ce gasar ta yara da matasa maza da mata ‘yan kasa da shekara 20 da ke da haddar Alkru’ani.

Dr.Kazaure ya ce yayin da maza ke gasar izu 60 na Alkur’ani, mata na yin izu 30 ne kuma za a kammala a alhamis din nan.

Daya daga limaman masallacin taraYya na Abuja Dr.Muhammad Kabir Adam ya ce ya na da muhimmanci duk iyaye su tabbatar ‘ya’yan su, na koyon karatun Alkur’ani don samun haddace shit un su na da karancin shekaru.

Dr.Adam ya ce shagaltar da yara da karatun Alkur’ani zai saita al’umma ta zama da albarka da kuma zaman lafiya.

Za a raba manyan kyautuka wadanda su ka fi kwazo dala dubu 5 ga kowanne da kujerar Makkah.