An Bude Gasar Cin Kofin Duniya A Afirka Ta Kudu

'Yan kallo fiye da dubu casa'in suka cika filin wasa na Soccer City a birnn Johannesbueg domin bukukuwan bude gasar cin kofin kwallon kafar duniya ta farko a nahiyar Afirka.

An fara gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta 2010, gasar da ita ce ta farko da aka taba kaiwa nahiyar Afirka. ‘Yan kallo kimanin dubu casa’in, akasarinsu sanye da kaya launin na ‘yan wasan Afirka ta kudu, watau rawaya da kore, sun cika filin wasa na Soccer City da aka gyara shi ful a birnin Johannesburg.

Mawaka da ‘yan rawa, wadanda suka sanya kayayyaki masu launi dabam-dabam, wasu ma suka yi fentin jikinsu, sun taka sosai a lokacin bude gasar.

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu da shugaba Felipe Calderon na kasar Mexico, sun zauna tare da juna su na kallon wasan farkon da a yanzu haka ake bugawa a tsakanin kasashensu biyu.

A bayan Afirka ta Kudu, akwai kasashen Afirka guda biyar dake wakiltar nahiyar a gasar bana, cikinsu har da Najeriya da Kamaru da Ivory Coast da Aljeriya da kuma Ghana.

Alhaji Isma’ila Ibrahim shi ne sakatare-janar na kungiyar magoya bayan Black Stars na Ghana. Yace dukkan ‘yan Ghana sun san matsayin kasar a tarihin Afirka, kuma a wannan karon ma su na sa ran rubuta wani sabon babin a Afirka ta Kudu. Ya ce, "...ina fada muku kamar yadda tarihin yake fadi, cewa Ghana ita ce kasar bakar fata ta farko da ta samu ‘yancin kai. Na san cewa Ghana ce kasar Afirka ta farko da zata kai ga akalla wasan karshe na cin kofin kwallon kafar duniya."

Sai dai kuma, Ghana ta shiga wannan gasa ba tare da shahararren dan wasanta Michael Essien dake buga ma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ba. Duk da haka, Maxwell Agyeman, yayi imanin cewa Ghana tana da kwararrun ‘yan wasan da zata iya taka rawar gani ba tare da Essien ba, yana mai cewa, "Ghana tana da shahararrun ‘yan wasa kamar Stephen Appiah da sauransu. Ina da kwarin guiwa sosai cewa zasu samu nasara. Duk da damuwar da wasu ke yi kan rashin Michael Essien saboda raunin da ya samu, Ghana zata taka rawar gani a wannan gasar."