An Bayyanar Da Sakamakon Zaben 'Yan Takara A Jihar Imo

Kenan yadda ta kaya a jihar Imo, a zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamna a tutar jam’iyyar APC mai mulki, inda shugaban sabon kwamitin gudanar da zaben, Malam Ibrahim Agbabiaka, ya ayyana Mista Uche Nwosu, surkin gwamna Rochas Okorocha, a matsayin wanda ya lashe zaben, biyo bayan soke zaben daya ga wata, inda tsohon kwamitin zaben dake karkashin jagorancin Alhaji Ahmed Gulak, ya ayyana cewa Sanata Hope Uzodinma ne ya lashe zaben.

Yanzu, a zaben da aka gudanar a duk fadin jihar jiya Asabar, Mista Uche Nwosu ya samu nasara ne da kuri’u 269,524 yayin da surkin gwamnan kuma, Injiniya Chuks Ololo ya biyo bayan Nwosu da kuri’u 6,428 Air Kwamanda Peter Gbujie mai ritaya ne yazo na uku da kuri’u 4,855 Sauran ‘yan takaran dai sun hada da Sir Jude Ejiogu, wanda ya samu kuri’u 3,456 da Barista Chima Anozie mai kuri’u 3,248 da Sanata Hope Uzodinma wanda ya samu kuri’u 2,729 da mataimakin gwamna, Prince Eze Madumere mai kuri’u 2,646 da kuma Mista Chris Nlemoha wanda ya samu kuri’u 955.

Shugaban jam’iyyar APC a jihar, Mista Daniel Nwafor kenan na cewa, “Zabe ne na gari aka gudanar, daya baiwa duk membobinmu a mazubu 305 na jihar damar shiga. Saboda haka, zabe na gari ne aka gudanar.”

Wasu daga cikin Hausawa mazaunan jihar sun bayyana ra’ayin su dangane da zaben a jihar ta Imo.

Yanzu, tun ranar Juma’a ne ‘yan takara 5, ciki har da mataimakin gwamna Prince Eze Madumere da Sir Jude Ejiogu, da Air Kwamanda Peter Gbujie mai ritaya, da Sir George Eche, da kuma Mista Chris Nlemoha, suka fice daga zaben, suna mai jaddada goyon bayansu ga Sanata Hope Uzodinma, kamar yadda kwamitin gudanar da zabe dake karkashin Alhaji Ahmed Gulak ya ayyana.

Sun kuma bukaci kotu ta hana jam’iyyar APC da hukumar zabe ta kasa (INEC) gudanar da sabon zaben fidda gwani na gwamna a jihar Imo.

Your browser doesn’t support HTML5

An Bayyanar Da Sakamakon Zaben Dan Takarar Jihar Imo 3'10"