Chelsea ta lashe gasar zakarun Turai sannan Ingila ta kai wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai, amma babu wani dan kasar Ingila da ke cikin jerin sunayen ‘yan takarar da FIFA ta fitar a ranar Litinin.
Jorginho, wanda ya kasance zakaran Turai sau biyu a Chelsea da Italiya, a tare da abokin wasansa N’Golo Kanté suna cikin 'yan takara 11 da za a zaba a matsayin gwarzon dan wasa na FIFA a wasar ta 2020-21.
Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun shiga jerin sunayen kamar yadda suka saba shiga da Robert Lewandowski wanda ya zama zakara bara.
Mohamed Salah, Kylian Mbappé, Erling Haaland, Kevin De Bruyne, Karim Benzema da Neymar suna cikin jerin sunayen da kwamitin da FIFA ta yanke.
Babu masu tsaron gida da ke jerin wadanda za a zabi zakara domin wannan babbar kyautar FIFA, ko da yake masu tsaron gida suna da tasu kyautar.
Gianluigi Donnarumma na Italiya, wanda aka zaba a matsayin gwarzon dan wasa a gasar Euro 2020, yana daga cikin ‘yan takarar masu tsaron gida biyar.
Za a tattara kuri'u daga kyaftin din tawagar kasar da masu horarwa, magoya baya da kafafen yada labarai na duniya har zuwa ranar 10 ga Disamba.
Za a gudanar da wani biki a ranar 17 ga Janairu ta hanyar intanet, daga hedkwatar FIFA da ke Zurich saboda cutar ta COVID-19.
Gwarzayen 'yan wasan maza na FIFA:
Karim Benzema (France / Real Madrid CF)
Kevin De Bruyne (Belgium / Manchester City FC)
Cristiano Ronaldo (Portugal / Juventus FC / Manchester United FC)
Erling Haaland (Norway / BV Borussia 09 Dortmund)
Jorginho (Italy / Chelsea FC)
N’Golo Kanté (France / Chelsea FC)
Robert Lewandowski (Poland / FC Bayern München)
Kylian Mbappé (France / Paris Saint-Germain)
Lionel Messi (Argentina / FC Barcelona / Paris Saint-Germain)
Neymar (Brazil / Paris Saint-Germain)
Mohamed Salah (Egypt / Liverpool FC)