An fitar da wani hoton bidiyo da ya nuna Mamaoudou Gassama yana kama karafan benen da hannuwansa yana hawa daga bene zuwa bene, yayinda wani mutum dake bene na hudu yake kokarin rike hannun yaron.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da kansa, ya godewa dan ci ranin jiya Litinin a fadar shugaban kasa ta Elysse, ya kuma bayyanashi a matsayin abin koyi.
Macron ya ba Gassama wanda ya fito daga yankin Keyes na kasar Mali lambar yabo ta nuna bajinta, ya kuma bashi takardar izinin zama dan kasa, da kuma aiki a ma'aikatar kashe gobara. Gassama ya shaidawa shugaban kasar cewa, "allah ne ya taimake ni" na ceto yaron.
Gassama yace shugaba Macron ya tambayeshi ya bayyana yadda ya yi wannan jarumtakar. Ya kuma ce ya nemi taimakon shugaban kasar ta Faransa.
yace "Na gaya mashi cewa cewa, na baro kasar Mali ta Burkina Faso, na shiga Nijar daga nan nabi ta hamada. Daga nan na isa Libya inda na yada zango na dan lokaci ina neman hanyar zuwa Italiya". Da farko nayi kokarin shiga jirgin kwale-kwale, sai hukumomi suka kama ni suka kulle ni a gidan yari daga nan suka tasa keyata zuwa Nijar. Sai na sake kwatantawa karo na biyu. Godiya ga Allah na samu na isa Ataliya.
Magajin garin birnin Paris Anne Hidalgo ma ta jinjinawa Gassama. Tace ba a nuna banbaci wajen sakama Gassama sabili da bajintarsa da yin tsayin daka kan batun shige da fice.
Ceto yaron
Mamoudou Gassama, dan shekaru 22 da haihuwa ya ce ya ga yaron na cikin mummunan hali a unguwar da ya je ranar Asabar don kallon wasan kwallon kafa a wani gidan saida abinci.
Gassama ya fadawa sashen Bambara na muryar Amurka cewa, sun yi odar abinci kenan shi da budurwarsa, sai suka ga mutane sun tattaru.
Yace “kafin mu fara cin abinci, na ga mutanen a waje. Wasu na ihu, direbobi kuma na ta latsa horn din mota. Sai na fita waje, na ga yaron yana lilo a bene na hudu, Gassama ya kara da cewa “na godewa Allah na iya kama karahuna ta gaban benen, na hau don in ceto shi, da na fara hawa karahunan, sai na kara samun kwarin guywar in ceto yaron.
Bayan da ya ceto yaron sai ‘yan sanda suka tare su ta wani daki, gassama ya ce “sai na fara makayarkyata, na kasa tsayawa, nayi ta rawar jiki saboda abinda ya faru.
Da farko ya fadawa CNN cewa yana son yara. Ba zan so in ga yaron ya ji rauni ba a gaban ido na. sai na ruga don neman hanyar da zan ceto shi. Na godewa Allah yadda na iya hawa ta gaban benen har na taddo yaron.
Rahotanni na nuni da cewa, iyayen yaron basu gida lokacin da lamarin ya faru. mahaifiyarshi tayi tafiya, yayinda aka ce mahaifinshi kuma ya tafi cefane. An kama mahaifin sabili da barin karamin yaron a gida shi kadai.