Ra'ayin Amurkawan ya saba matsayin 'yan takarar da suke kan gaba na jam'iyyar Republican a zaben Amurka da za'a yi badi.
Kamfanin Gallup ya gudanar da wannan kuri'ar ce cikin watan Yuni, inda ya tambayi masu zabe ko zasu amince da dan takarar da yake bin darikar katholika, ko ba yahude, ko dan darikar Mormon wata darikar addinin kirista, da 'yan bishara, ko musumi ko ma wanda bai yarda da Allah ba. Kuri'ar neman jin ra'ayin jama'ar ta nuna goyon baya ga wadannan rukoninin mabiya daga kashi 93 cikin dari ga mabiya darikar katholika zuwa kashi 58 cikin dari ga wadanda basu ma yarda da Allah ba.
A ranar Lahadi data gabata ne tsohon likitan nan na Laka data hada da kwakwalwa anan Amurka Ben Carson, wanda yanzu yana daga cikin wadanda suke kan gaba a neman takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican, ya gayawa shirin tashar NBC da ake kira Meet the Press, cewa shi ba zai goyi bayan a zabi Musulmi shugaban Amurka ba.
Tsarin mulkin Amurka dai ya hana auna addinin mutum a zaman matakin zabensa shugaban kasa koma wasu mukamai. Nan da nan aka yi Allah wadai da matsayar Ben Carson. Majalisar Musulmi ta Amurka tace bai cancanci zama shugaban Amurka ba, daga nan tayi kira gareshi daya janye daga takara.
Jiya Talata Carson ya zargi siysa ce ta jawo cece kucen da ya biyo bayan kalamansa.