Ranar 21 ga watan Agusta jihohin Amurka 50 baki daya sun sha kallon husufin rana, abinda ya baiwa daukacin al'umar Amurka damar ganin yadda wata ya shiga tsakanin duniyar dan'adam da kuma duniyar rana.
WASHINGTON DC —
Hakan ya sa inuwa ta shige laimar duniyar mu. Yanayin abunda zai wakana ya danganci inda mutane suke. Idan kana hanyar da husufin zai auku sosai, zaka kalli yadda wata baki dayansa zai rufe rana. Idan kuma kana wajen hanyar husufin, zaka kalli wata zai wuce rana, amma bai zai rufe rana baki daya ba.
An dai umurci mutane da cewa ko ina suke kada su kalli rana kai tsaye ba tareda madubi na musamman domin kallon husufin ba. Amma ind a zaka iya kallo ba tareda madubi na musamman ba shine idan wata ya rufe ranar baki daya. Ba safam irin haka ke faruwa ba.
Rabon Amurka da husufin rana da zai shafi kasar baki daya tun a shekarar 1918, sannan husufin rana nan gaba ba zai auku ba sai a shekara ta 2024.
Your browser doesn’t support HTML5