An sami saukin saukar dusar kankarar a yankin birnin Washington, inda yawancin yankunan babban birnin suka samu dusar kankarar da takai santimita 60. A dalilin wannan guguwa ne aka rufe ofisoshin gwamnati da ke birnin, jami’ai ma suka rufe manya da kananan hanyoyi, harma da ‘daukacin sashen sufuri na birnin.
Masu hasashen yanayi sunce an samu yawan dusar kankarar da ta sauka a jihar New York mai hawan santimita 64.
Gwamnan jahar New York Andrew Cuomo ya kafa dokar hana tafiye-tafiye a dukkannin hanyoyin unguwanni da manyan hanyoyin da ke birnin mai yawan mutane miliyan 8.4. An dakatar da zirga zirgar ababen hawa, da rufe shaguna da duk wasu wasu guraren more rayuwa.
Fiye da mutane miliyan 85 wannan guguwar karfi hade da dusar kankarar ta shafa, inda ta bar dubban mutane zama cikin duhu a dalilin katsewar wutar lantarki.