Amurkawa Na Tanadin Abinci Saboda Guguwar Dorian

Yadda aka saye burodi a wani shago a wani kantin jihar Florida a Amurka

“Muna kira ga daukacin mazauna jihar Florida da su tanadi abincin kwanaki bakwai da magunguna da ruwa.” In ji gwamnan jihar ta Florida Ron DeSantis.

Cibiyar da ke sa ido kan aukuwar bala’in guguwa ta Amurka, ta ce karfin guguwar da aka wa lakabi da "Dorian" ta kai mataki na 4, matakin da ta ce, ya kai mai “hadarin gaske.”

Ya zuwa yanzu rahotanni sun ce guguwar ta doshi yankin Bahamas da wasu yankunan jihar Florida a nan Amurka.

“Muna kira ga daukacin mazauna jihar Florida da su tanadi abincin kwanaki bakwai da magunguna da ruwa.” In ji gwamnan jihar ta Florida Ron DeSantis.

Su ma dai hukumomin Bahamas, sun fidda gargadi ga yankin arewa maso yammaci, yayin da Shugaba Donald Trump shi ma ya ayyana dokar ta-baci a daukacin jihar ta Florida.

Cibiyar da ke sa idon kan aukuwar bala’in guguwar a Amurka, ta ce saboda yanayin yadda guguwar ke tafiya a hankali, za a kwashe tsawon lokaci ruwan sama na zuba, lamarin da zai haifar da yanayi na bala’in ambaliyar ruwa mai barazana ga rayuwa.