Dan takarar Shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican mai jiran ayyanawa Donald Trump, ya ce shi fa dan takara ne mai jaddada bin doka da oda, a jiya Litini, ya ce dole ne fa Amurkawa su kawo karshen yin fito na fito da 'yansanda, a kuma kyautata rayuwar jama'a a biranen da aka cika aikata laifuka.
"Amurkawa da dama na cikin firgici da tashin hankali da kuma fatara," abin da hamshakin attajiri mai harkar gine-ginen ya fada a wurin yakin nemar zabensa a birnin Virginia Beach da ke jahar Virginia.
Ya yi wannan jawabin ne yayin da Amurkawa ke cigaba da jin radadin tashe-tashen hankulan da su ka faru makon jiya, lokacin da 'yansanda su ka harbe wasu Amurkawa Bakaken fata biyu har lahira - daya a Lousiana dayan kuma a Minnesota - 'yan kwanaki kafin wani dan bindiga Bakar fata ya auna 'yansanda farar fata, a wata ramuwar gayya a Dallas, jahar Texas, ya bindige 'yan sanda biyar har lahira.
Trump, wanda ke gab da zama dan takarar Shugaban kasar jam'iyyarsa a hukumance a babban taron jam'iyyar da za a yi a makon jiya, ya ce,
"'Yansandanmu na rugawa zuwa wurare masu hadari kulluyaumin don su kare al'ummominmu kuma akasari su kan yi hakan ne ba tare da an gode masu ba, a maimakon hakan ma sai suka. Muna goyon bayanku kuma har kullum, har kullum, har kullum zamu goyi bayanku," in ji shi.