Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Venezuela Na Shiga Kasar Colombia Neman Kayan More Rayuwa


Wasu 'yan Venezuela rike da yakan da suka sawo daga Colombia
Wasu 'yan Venezuela rike da yakan da suka sawo daga Colombia

Dubban ‘yan kasar Venezuela sun ketara kan iyakar kasar domin shiga kasar Colombia a jiya Lahadi, da nufin sayo kayayyakin masarufi da na more rayuwa, da su ke da matukar wahalar samu a kasarsu, saboda matsin da tattalin arzikin kasar ya shiga, wanda ya haifar da karancin kayyakin.

Da dama daga cikin ‘yan kasar sun yi tuki na sa’oi masu tsayi, domin cin amfani da damar bude kan iyakar da hukumomin kasar suka bayar ta sa’oi 12, tsakanin Tachira da ke Venezuela da Cucuta da ke Colombia.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, ya sa an rufe kan iyakar kasar a bara saboda dalilai na tsaro, amma ya kuma ba da damar a bude kan iyakar a jiya Lahadi.

Wasu suna sayarwa 'yan Venezuela kaya a bakin iyaka da kasar Colombia
Wasu suna sayarwa 'yan Venezuela kaya a bakin iyaka da kasar Colombia

Hakan kuma ya baiwa ‘yan kasar damar sayo kayayyakin da dama daga Colombian, wadanda su ke da matukar wahalar samu ko kuma saya a Venezuela, kamar kayyakin da suka hada da garin fulawa da mai da magunguna da dai sauransu.

A makon da ya gabata, daruruwan ‘yan kasar ta Venezuela sun yi ta shiga kasar ta Colombia ta harmatacciyar hanya, domin neman wadannan kayayyaki.

An dai dora karancin wadannan kayayyaki akan fadin farashin man fetur a kasuwannin duniya, wanda ya shafi kasar matuka, saboda ta kan shigar da dukkanin kayayyakin da ta ke amfani da su ne daga waje.

XS
SM
MD
LG