Amurkawa duk fadin kasar na bikin samun 'yancin kasar. Tun shekara 1941 aka fara kebe ranar 4 ga watan Yulin a matsayin ranar gudanar da shagulgulan wannan rana.
WASHINGTON, D.C. —
Yau Talata 4 ga watan Yuli ana bukukuwan murnar samun 'yancin kai da Amurka ta yi.
Ranar biyu ga watan Yulin 1776, majalisar kasa ta kada kuri’ar amincewa da kebe ranar samun ‘yancin kai.
Bayan kwana biyu, wakilai daga gundumomin Amurka 13 suka amince da kudurin 'yancin da Thomas Jefferson ya rubuta.
Wadansu masana tarihi suna ganin kamata ya yi ranar bukin ‘yancin kan Amurka ta kasance ranar biyu ga wata a maimakon hudu ga wata, domin ranar ce aka kada kuri’a ta tarihi.
Yanzu a Amurka, dubban al’ummomi suna shirya wasanni wuta domin bukin wannan ranar.
Ana gudanar da daya daga cikin manyan wasan wutan a gundumar Columbia babban birnin kasar da aka fi sani da Washington DC.