Amurka zata tura karin daruruwan dakarunta da kayan yaki kasar Saudiyya don dakile wani yinkurin tsokana daga Iran.
Sakataren harkokin tsaron Amurka Mark Esper ya fadawa manema labarai jiya Jumma’a cewa cikin abubuwan da za a tura har da jiragen saman yaki guda biyu na Fighter Squadrons, da karin makamai masu linzame, da na’urar kariyar makamai masu linzame da ake kira THAAD a takaice, da kuma jami’an sojan da zasu taimaka.
Kusan dakarun Amurka 3,000 aka tura kasar Saudiyya tun bayan wani hari akan masana’antun sarrafa man Saudiyya a watan da ya gabata da aka dora laifin akan Iran. Jami’an Amurka sun ce daga kudu maso yammacin Iran jiragen da suka kai harin suka fito, amma Tehran ta musanta zargin.
Esper ya ce Amurka ta tura karin sojojinta guda 14,000 zuwa yankin tun daga watan Mayu, a lokacin da aka kaiwa wasu tankokin mai guda 4 hari a yankin. Haka kuma an dorawa Iran da dakarun dake samun goyon bayan Iran din laifin wasu hare-hare akan wasu tankokin mai a watan Yuni, da kuma harbo jiragen saman Amurka marasa matuki.