A lokacin da ya kamala ziyararsa ta kwanaki uku da ya kai a Gabas ta Tsakiya, Pence ya fadawa kampanin dillancin labarai na Reuters cewa, fadar White House tana tattaunawa da kawayenta na yankin ko zasu iya fitowa da tsarin tattaunawar zaman lafiyar. Amma dai hakan zai tabbata ne bisa amincewar Falasdinu na komawa ga teburin tattaunawar.
Wani babban jami’in Fadar White House ya fadawa manema labarai a birnin Kudus cewa, masu tattaunawa na bangaren Amurka basu kayyade lokacin kamala tattaunawar ba, saboda a baya cimma lokacin da aka kayyade ba.
Bangarorin zasu dace a kan lokacin da suka amince su fara tattauanawar, inji jami’in na White da ya bukaci a sakaya sunansa.
Pence ya fada a hirarsa da Reuters cewa, shi da shugaba Donald Trump, sun yi imanin shawarar dauke ofishin jakadancin Amurka daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Kudus zai taimaka ainun wurin cimma tattaunawar zaman lafiyar yankin.