Amurka Zata Dakatar Da Shirin Bada Mafaka Ga Baki

Gwamnatin shugaba Trump na shirin hana yawancin masu neman mafaka a kudancin iyakar kasar, da ke shigowa Amurka, matakin da zai fi shafar ‘yan yankin Amurka ta tsakiya da suka ketaro ta cikin Mexico.

Matakin gwamnatin, wanda ma’aikatar shari’a da ta tsaron cikin gida na Amurka suka sanar, ya hana mutane neman mafaka a Amurka idan sun bi ta wata kasa da ke bada mafaka kafin suka iso Amurka, a cewar wata takardar gwamnatin tarayya mai shafi 58 da aka wallafa jiya litinin.

A wata sanarwa, Atoni Janaral na Amurka William Barr, ya bayyana cewar ana samun karuwar baki dake isa bakin iyakar Amurka da Mexico sosai, ya kara da cewa kadan daga cikin wadannan mutanen ne suka cancanci samun mafaka.