Amurka Za Ta Tura Sojoji Zuwa Kan Iyakarta Da Mexico

Bakin haure daga kasashen tsakiyar nahiyar Amurka da suka sha alwashin shiga kasar Amurka lamarin da ya bata wa Shugaba Trump rai

Takobin da bakin haure daga kasashen dake tsakiyar nahiyar Amurka suka lasa sai sun shiga kasar Amurka ya sa Shugaba Trump na shirin aika sojoji kan iyaka da kasar Mexico

Amurka zata tura sojoji zuwa kan iyakarta da Mexico domin dakile kwararar bakin haure zuwa kasar, shugaban Amurka Donald Trump ya gayawa manema labarai haka jiya Talata.

Shugaban tare da yawa cikin ministocinsa, ciki harda ministan tsaro James Mattis, Ministan kula da tsaron gida, Kirsten Nielson, da Atoni Janar Jeff Sessions, sun saurari bayanai kan manufar gwamnatin Trump na daukar wannan mataki. Shawarwarin sun hada da tura dakarun kasa da ake kira National Guard, da kuma bukatarmatsawa majalisun dokokin tarayya su zartas da doka da zata toshe duk wata hanya da masu bakar aniya masu safarar mutane 'yan ta'ada da 'yan fasa kwauri zasu iya yin anfani da ita.

Ma'aikatar tasaron Amurka da ake kira Pentagon ta ce tana ci gaba da tuntubar fadar White House kan wannan mataki.

Tsoffin shugabannin Amurka George W. Bush da Barack Obama sun tura dakarun tsaron kasa da ake kira National Guard zuwa kan iyaka inda suka taimaka da tattara bayanan sirri da sintiri da jirage a zaman tallafi ga jami'an dake tsaron kan iyakokinta.