Gwamnatin Amurka karkashin Shugaba Donald Trump, za ta takaita yawan ma’aikatan kafafen yada labarai na gwamnatin China da su ke Amurkar.
Wannan shawarar da Amurka ta yanke na zuwa ne, bayan da kungiyar wakilan kafafen yada labarai na kasashen waje da ke China (FCCC) ta wallafa rahotonta na shekara-shekara mai manufar kare ‘yancin jaridanci.
Rahoton ya bayyana nau’ukan musguna wa, da takura wa da kuma kokarin kada ‘yan jarida yadda ta ga dama da China ke yi.
To amma wani mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China, mai suna Zhao Lijian ya yi watsi da rahoton kungiyar ta FCCC.
Ya ce, “Ba mu taba ma kula da wannan kungiyar da aka ambata ba, rashin kaifin hankali da kuma rashin sanin ya kamata ne ke damunta. Ya za ta tashi kwatsam ta ce wai za ta sasanta tsakanin jam’iyyun siyasa, sannan kuma ta goyi bayan bangare guda. Har kullum kasar China na maraba lale da kafafen yada labarai na kasashen waje, muddun za su ba da rahoto kan China cikakke kuma bisa gaskiya."
Amurkar na mai nuni da cewa ta dauki wannan matakin ne don yawan tsangwama da barazana ga ‘yan jarida da aka san China da yi tun da dadewa.