Amurka Za Ta Taimakawa Nigeria Ta Gudanar Da Zaben 2019

Jakadan Amurka a Nigeria Stuart Symington

A cewar jami'in dake hulda da jama'a a ofishin jakadancin Amurka dake Abuja, kasar ta Amurka za ta taimakawa Nigeria domin ta tabbatar an gudanar da zaben 2019 cikin kwanciyar hankali

Kasar Amurka ta bada tabbacin taimakawa Nigeria wajen ganin an gudanar da zaben kasar na shekarar 2019 cikin lumana da walwala.

Shugaban sashen hulda da jama'a a ofishin jakadancin Amurka dake Abuja Mr. Aruna Amirthanayagam, shi ya tabbatar da hakan a wata ziyarar aiki da ya kai jihar Niger. Yace Amurka ta hada hannu da Nigeria wajen gudanar da shirye shiryen ci gaban al'ummar kasar, musamman ta fuskar ilimi, kiwon lafiya da tsaro.

Jami'in na ofishin jakadancin Amurka ya ce kasarsa a shirye take ta ba da duk wata gudummawar da ta wajaba domin ganin babban zaben kasar ya gudana lafiya.

Dangane da batun yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Buhari ke yi, ya ce an samu ci gaba amma akwai bukatar kara kaimi saboda haka "za mu ba da gudummawa da abun da za mu iya bayarwa" inji Mr. Amirthanayagam.

A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari domin karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Amurka Za Ta Taimakawa Nigeria Ta Gudanar Da Zaben 2019 Lafiya - 2' 39"