Najeriya ta kulla yarjejeniyar cinikayya da babban kamfanin kera jiragen sama mai suna Boeing domin tabbatar da kudurin Shugaba Buhari na sake kafa sabun kamfanin sufurin jiragen sama na kasa.
Ana sa ran wanda za a kafa yanzu ya fi wanda aka taba yi a da na Nigerian Airways, inji Minisitan Sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika a wata zantawa da ya yi da Muryar Amurka.
Ministan ya tabbatar da yiwuwar wannan yunkurin da kamfanin Boeing inda ya bayyana cewa,
" Kamfanin ya ci alwashin cewa idan har Najeriya na da bukata - wacce kuma muna da, kuma mun kakkabe takardunmu, mun gyarasu kan abinda ya kamata, to in Allah ya yarda za su bamu hadin kai, zasu bamu jiragen da zamu kafa wannan kamfanin (jirage na kasa) da shi." inji ministan
Sai dai a cewarsa, wannan kamfanin zai banbanta da na da, inda a wannan karo masu hannu da shuni, da kamfanoni na ciki da waje ne su za su hada hannu a yi shi, ita kuma gwamnati ta bayar da tallafi.
Kamfanin Boeing na daukar shekaru 4 zuwa biyar kafin su gama kera jiragen da aka basu a cewar ministan.
"Amma saboda martabar Shugaba Buhari da muhimmancin ziyarar da ya kawo, kamfanin ya amince zai bamu jiragen da muke bukata da wuri-wuri."
Sai dai yaushe ne wannan sabon kamfanin zai fara aiki? Ministan ya bayyana cewa daga nan zuwa watan Yulin wannan shekarar za su yi sanarwar inda aka kwana.
Saurari cikakken hirar da Aliyu Mustapha yayi da ministan.
Your browser doesn’t support HTML5