ACCRA, GHANA - Makasudin taron na wannan shekarar shi ne bunkasa kasuwanci da zuba jari, tare da samar da dama tsakanin kamfanonin Amurka da Ghana, da kuma nazarin masana'antu da na'urorin zamani a matsayin hanyoyin da za su tabbatar da tsarin kasuwa daya a nahiyar Afirka.
Da yake jawabi a wajen taron kasuwancin tsakanin Amurka da Ghana na shekarar 2022, wanda aka yi wa taken "Yin Amfani da yarjejeniyar kungiyar AfCFTA don inganta haɗin gwiwar kasuwanci tsakanin Amurka da Afirka" wanda kungiyar 'yan kasuwar Amurka a Ghana ta shirya, Don Graves ya ce Amurka za ta ci gaba da karfafa huldar kasuwanci da Ghana domin taimaka wa kasashen biyu su samu ci gaba.
“Zan so a samu dangantakar kasuwanci mai karfi. Ina fatan za mu iya amfani da dala biliyan 2.7 ko kusa da haka kuma mu ninka kudin cikin shekaru biyu ko uku sannan mu sake ninka su cikin 'yan shekaru kadan masu zuwa.”
Graves ya kuma ce ya kamata a ci gaba da hulda tare domin cimma burin gyara harkokin kasuwanci ta yadda ‘yan Amurka da ‘yan Ghana za su samu saukin tattauna wa da hukumomin juna a kan kasuwanci.
Ya kara da cewa Amurka za ta karfafa wa 'yan kasuwarta gwiwa akan harkar kasuwanci a Ghana tare da zuba hannun jari, hakan zai sa matasa da yawa su samu aikin yi.
A hirarsa da Muryar Amurka, masanin tattalin arziki, Hamza Adam Attijanny, ya ce Ghana ce kasa ta biyu da kasar Amurka ta fi yin kasuwanci da ita, kuma bude sabon bankin ci gaban Ghana da aka yi kwanan nan zai taimaka wajen cimma burin kara dankon alakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Taron ya samu halartar jami'an gwamnati daga kasashen Ghana da Amurka, da shugabannin kasashen da ke karkashin AfCFTA, da 'yan kasuwa, da hukumomin harkokin cinikayya. Ministan Kudin Ghana Ken Ofori-Atta da Ministar Sadarwa, Ursula Owusu-Ekuful su ne manyan baki a wajen taron.
Saurai rahoto cikin sauti daga Idris Abdullah:
Your browser doesn’t support HTML5