Amma zata fara tattaunawa domin ko dai ta sake shiga yarjejeniyar ko kuma wata sabuwar yarjejeniya baki daya. Bisa sharuddan da suka dace da Amurka, da al’ummarta da kuma masu biyan harajinta.
A jawabin da yayi a fittacciyar harabar bangaren fadar White House da ake kira Rose Garden, Trump yace yarjejeniyar bata da wani tasiri kan yanayi, banda haka kuma, tana gallazawa Amurka ne ta wajen gindaya mata sharuda masu tsauri fiye da kasashen da suka fi gurbata muhalli.
Amurka zata janye daga yarjejeniyar yanayi ta birnin Paris amma zata fara tattaunawa domin ta sake shiga, ko dai yarjejeniyar ta Paris,ko kuma wata sabuwar yarjejeniya da ta kyautatawa Amurka, da cibiyoyin kasuwancinta da ma’aikatanta, da al’ummarta da kuma Amurkawa masu biyan haraji.
Shugaba Trump ya bayyana haka ne duk da rashin amincewar da shugabannin kasashen duniya da kuma na kamfanoni suka nuna, wadanda da dama suka roki shugaba Trump baki da baki kada ya janye daga yarjejeniyar.