A cewarsu wannan mataki ya yi daidai domin zai kara karfafa dangantakar kasashen biyu, suka kuma yi kira ga sauren kasashen yankin Gabas Ta Tsakiya da su kara zage dantse wajen taka rawar-gani a yakin da ake yi da kungiyar IS.
Tsohuwar Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, wacce ke gaba-gaba a karbuwa a karkashin jam’iyar ta Democrats, ta ce akwai bukatar a kara daukan wasu matakai domin daidai dangantaka da kasar ta Iran, amma kuma ta ce Amurka na bukatar ta tursasa Iran din ta gujewa irin mummunar rawar da ta ke takawa a Syria.
Shi kuwa Bernie Sanders, wanda ke kokarin kamo Clinton a karbuwa a ‘yan watannin nan, cewa ya yi matsayar da aka cimma da Iran ba tare da an yi yaki ba “abu ne mai kyau” sai dai ya ce kada a yi hanzarin bude ofishin jakadancin Amurkan a birnin Tehran.