Amurka: 'Yan Republican dake neman shugabanci kasa sun yi muhawara ta shida

'Yan Republican da suka yi muhawara jiya Alhamis

A siyasar Amurka 'yan takara kowace jam'iyya sai sun yi watanni suna muhawara tsakaninsu da nufin tallata kansu kafin su tsaya takarar fidda gwani da zai zama wakilin jam'iyyarsu da zai fafata da duk wanda jam'iyyar Democrat ta tsayar

'Yan takara 16 suka fito neman jam'iyyarsu ta Republican ta tsayar dasu takarar zaben shugaban kasa.

Bayan muhawarori biyar kafin na jiya wadanda basu sami karbuwar jama'a ba sun fice saboda haka 'yan takara biyar ne kawai suka yi muhawara jiya.

Wadan nan bakwai din kuwa su ne Donald Trump, Jeb Bush, Ted Cruz, Marco Rubio da Chris Christie. Tana yiwuwa nan gaba wasu cikinsu su fice.

Ba tare da bata lokaci ba 'yan takarar suka shiga caccakar juna akan harkokin kasashen waje, tattalin arziki da kuma bakin haure.

Muhawarar ta jiya da suka yi a jihar South Carolina nada mahimmanci domin nan da makonni uku ne jam'iyyar zata fara zaben fida gwani a jihohi.

Jeb Bush da ya fara magana ya caccaki Donald Trump akan nufinsa na hana musulmai da ba amurkawa ba ne shiga kasar. Jb Bushi yace matsayin Trump akan musulmai ba zai haifi da mai ido ba, maimakon haka ma zai kara harzuka mayakan sa kai na kungiyar ISIS

Da yake mayarda martani Trump yace tsaron Amurka ne ya fi damunsa. Yace kasar tana da matsala da musulmai masu tsatsatsauran ra'ayi. Matsalar ba ta Amurka ba ce kadai ta duk duniya ce.

Muhawarar ta dauki zafi yayinda Ted Cruz ya tabo batun zama dan kasa da ya cancanta ya tsaya takarar zaben shugaban kasa. Yace tun fil azar dokar Amurka ta amince wa dan ba'amarike da aka haifa waje zama cikakken dan Amurka.

Trump bai yi watawata ba sai ya fadawa Cruz ya shirya domin za'a kaishi kara kuma wa ya sani ko za'a barshi ya shugabanci kasar. Saboda haka ya tafi ya shirya domin babu yadda zai tsira tunda ba akasar aka haifeshi ba.

Muhawarar ta cigaba da kalamu masu zafi. Babu mamaki 'yan takaran sun yi magana da kakkausan lafazi saboda zaben fidda gwani ya karato.